Rundunar ‘yansandan jahar Kano ta kama wani sojan-gona wanda ake zargi da kwarewa wajen karbe kudade a hannun masu a daidaita sahu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Kano ranar Talata.
Ya ce wanda ake zargi da sojan-gonan sunansa Abubakar Zailani Ibrahim, mai shekaru 27, kuma yana gabatar da kansa a matsayin soja, inda ya kama wani mai a dai-daita sahu ya kai zuwa ofishin ‘yansanda na Rijiyar Zaki a Kano.
Haruna Kiyawa ya sanar da cewa kwamishinan ‘yansanda, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya umarci DPO na Rijiyar Zaki, Usman Abdullahi, ya binciki lamarin.