For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

‘Yansanda Sun Kama Wani Da Sassan Jikin Mutum A Zamfara

Jami’an ‘yansanda a Jihar Zamfara sun kama wani da ake zargi da kashe mutane da kuma mallakar sassan jikinsu.

Sanarawar da Rundunar ‘Yansanda Zamfara ta fitar a jiya Litinin ta baiyana sunan wanda ake zargin da Jabiru Ibrahim da Dauran a karamar hukumar Zarmi da ke jihar.

“An kama wanda ake zargin ne ta hanyar hadinguiwar ‘yansanda da sojoji a yankin Dauran-Zurmi, kuma an kawo shi Helkwatar ‘Yansanda da ke Gusau domin fadada bincike,” in ji mai magana da yawun rundunar, Mohammed Shehu.

“Binciken farko ya nuna cewa, wanda ake zargin daya ne daga cikin rusassun gungun mutanen ne da ake kira da YANSAKAI wadanda suke tayar da hankalin mutanen Dauran ta hanyar yi musu hukuncin kai tsaye (jungle justice), abinda yake jawo mayar da martanin ‘yan bindiga kan wadanda ba su ji ba ba su gani ba.

“A lokacin da ake yiwa wanda ake zargin tambayoyi, ya amsa laifinsa tare da baiyana wasu mutum uku da yake aiki tare da su, wadanda ba a kama su ba, cewar sun kashe wani Bafulatani da ake kira da Abdullah, sannan daga baya wanda ake zargin ya cire hannun dama na mamacin.”

Ana dai ci gaba da bincike kan lamarin domin kamo abokan aikin nasa da kuma binciko dalilansu na aikata laifin kafin a mika su kotu.

Comments
Loading...