For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

‘Yansandan Najeriya Za Su Fara Karbar Sabon Karin Albashi A Janairun 2022

Majalisar Zartarwar Kasa ta amince da karawa jami’an ‘yansanda albashi da kaso 20 cikin 100.

Ministan Ma’aikatar ‘Yansanda, Maigari Dingyadi, ya bayyana hakan ne a yau, bayan kammala zaman majalisar zartarwar wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, a fadarsa dake Abuja.

KU KARANTA:

Ministan ya ce ana sa ran sabon karin albashin zai fara aiki daga watan Janairu na shekarar 2022.

Kazalika, Majalisar Zartarwar ta amince da kashe Naira Biliyan 13.100 domin biyan hakkokin ‘yan sanda dubu 5,472 wanda suka mutu a lokacin da suke bakin aiki daga shekarar 2013 zuwa 2020.

Comments
Loading...