For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Yanzu Mu Muke Da Cikakken Iko Da Jihar Rivers – PDP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP ta bayyana cewar ita ke da cikakken iko da Jihar Rivers, inda tai alfaharin cewa, Gwamnan jihar Siminalayi Fubara da jam’iyyar ke riƙe da madafun ikon siyasar jihar.

A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar na Ƙasa, Debo Ologunagba ya saki a yau Asabar, jam’iyyar ta bayyana cewar dukkan ‘yan majalissar jihar da suka fice daga jam’iyyar suka koma jam’iyyar All Progressives Congress sun rasa kujerunsu, inda ta kafa hujja da tanadin dokar kundin tsarin mulki.

A ranar Talatar da ta gabata ne, rahotanni suka nuna cewar Gwamnatin Jihar Rivers ta yi watsi da kiran da kwamitin riƙo na APC yai ga ƴan majalissar jihar na su tsige gwamnan jihar Fubara.

Jam’iyyar PDP ta jaddada cewar, a yanzu tsarin doka ya ba ta cikakkiyar nasara, inda tai allawadai da kiran APCn tare da bayyana shi amatsayin yunƙurin yi wa kundin tsarin mulki hawan ƙawara.

PDPn ta ce, duba da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, dukkan ƴan majalissar da suka sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a yanzu haka tsofin ƴan majalissa ne.

Ta ƙara da yin kira ga APC da ƴan majalissar da su yi watsi da tunanin cewar jam’iyyar zata karɓi iko a Jihar Rivers.

Comments
Loading...