Gwamnatin Tarayya da haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago sun cimma matsaya kan cewa, ƙarin mafi ƙarancin albashi na naira 25,000 da Tinubu ya sanar a jawabinsa na yau ya haɗa da dukkan wani ma’aikaci a Najeriya.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewar za ta nemi ra’ayin rassanta na ƙasa a gobe Litinin domin jin ra’ayinsu kan abubuwan da aka cimma a zaman sirrin da ƙungiyar ta yi da Gwamnatin Tarayya a yammacin yau Lahadi.
Shugaban Ƙungiyar NLC, Joe Ajaero da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila ne suka yi jawabin bayan zaman da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Akwai ƙarin bayani . . .