For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

YANZU-YANZU: Ƙungiyar Ƙwadago Na Zama Da Gwamnati A Villa

Gwamnatin Tarayya da Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago yanzu haka na zaman tattaunawa a Ɗakin Taron na Ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa da ke Villa a Abuja.

Zaman na yau Litinin an tsara shi ne, domin wakilan ƙungiyoyin ƙwadago su gabatarwa da gwamnati matsayar ƴan Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, da ƴan Ƙungiyar Ƴan Kasuwa, TUC, suka yanke game da abubuwan da gwamnati da gabatar musu a jiya.

A cikin hukuncin na ƴan ƙwadagon ana sa ran jin matsaya kan shiga yajin aikin sai baba-ta-gani da suke shirin farawa gobe.

An gano cewar ɓangaren gwamnatin na yin zaman ne a mabanbantan lokuta da ƴan ƙwadagon, inda a yanzu take zama da ƴan ƙungiyar TUC kafin daga bisani ta zauna da ƴan ƙungiyar NLC.

Comments
Loading...