Mutanen da ba su gaza 6 ba ne aka harbe har lahira a yankin Sabo da ke garin Ondo a Jihar Ondo a jiya Laraba da daddare, harin da ake zargin ƴan bindiga da kaiwa.
Wannan ya faru ne awanni 72 bayan wasu ƴan bindigar sun kai hari St. Francis Catholic Church, da ke Owo, inda aka kashe mutane 40.
Wasu da dama cikin masu ibada a cocin kuma sun ji raunuka.
An rawaito cewa, ƴan bindigar suna kan baburane lokacin da suka kai harin.
Wata majiyar kuma ta ce, ƴan bindigar sun kuma yashe shaguna da yi wa mutane fashi kafin su bar yankin.
Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar Ƴansandan Jihar, Mrs Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ta kuma ce, fashi ne aka yi, inda ta ƙara da cewa, jami’ai a rundunar sun garzaya domin bin bayan masu laifin.