Waɗansu da ake zargin ƴan ta’adda ne sun tashi bom a kan titin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna, kuma sun sami nasarar karya titin.
Wata majiya mai inganci ta tabbatar da faruwar lamarin a daren yau Litinin.
A lokacin da aka kai harin akwai mutane 970 a cikin jirgin.
Wasu majiyoyi sun sanar da NIGERIAN TRACKER cewa an yi garkuwa da fasinjoji da dama sannan kuma da dama sun ji raunuka.
(NIGERIAN TRACKER)