For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

YANZU-YANZU: Ƴan Ta’adda Sun Tayar Da Bom A Kan Titin Jirgin Ƙasa Na Abuja-Kaduna

Waɗansu da ake zargin ƴan ta’adda ne sun tashi bom a kan titin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna, kuma sun sami nasarar karya titin.

Wata majiya mai inganci ta tabbatar da faruwar lamarin a daren yau Litinin.

A lokacin da aka kai harin akwai mutane 970 a cikin jirgin.

Wasu majiyoyi sun sanar da NIGERIAN TRACKER cewa an yi garkuwa da fasinjoji da dama sannan kuma da dama sun ji raunuka.

(NIGERIAN TRACKER)

Comments
Loading...