Shugabannin Jam’iyyar APC na Kasa sun goyi bayan matsayar gwamnonin jam’iyyar na yankin Arewa kan batun mika takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar zuwa yankin Kudu.
Gwamononin Arewan dai sun matsa kan batun mika takarar Shugaban Kasar zuwa yankin Kudu, bayan fitowarsu daga ganawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau Litinin.
Wannan na zuwa ne duk da sanar da sunan Shugaban Majalissar Dattawa a matsayin dan takarar Shugaba Muhammadu Buhari, kamar dai yanda Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Abdullahi Adamu ya sanar.
Abdullahi Adamu ya yi sanarwar ne a zaman shugabannin jam’iyyar na kasa wanda aka gudanar yau a Abuja.
To sai dai kuma, Sakataren Tsare-Tsare na Kasa na Jam’iyyar APC, Suleiman Argungu ya ce, zabar Ahmad Lawan a matsayin dan takarar masalaha ra’ayin Abdullahi Adamu ne shi kadai.
Argungu ya ce, shugabannin jam’iyyar na kasa, suna goyon bayan matsayar gwamnonin jam’iyyar ne na Arewa kan mika takara zuwa Kudu.
Ya ce zabar Shugaban Majalissar Dattawa a matsayin dan takarar maslaha ba ra’ayin shugabannin jam’iyyar ba ne, sai dai kawai ra’ayin Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Abdullahi Adamu.
“Kawai labari ne da Shugaban Jam’iyya ya fada. Kwamitin Shugabancin Jam’iyya yana goyon bayan matsayar gwamnonin Arewa ne, ta mika mulki zuwa Kudu,” in ji Argungu.