For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

YANZU-YANZU: Alƙalin Kotun Ƙolin Najeriya Ya Rasu

An rawaito cewa, Justice Chima Centus Nweze na Kotun Ƙolin Najeriya ya rasu a jiya Lahadi yana da shekaru 64 a duniya.

Har kawo yanzu dai Kotun Ƙolin ba ta sanar da mutuwar alƙalinba a hukumance.

In za a iya tunawa, Justice Nweze ne ya bayyana Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Imo na shekarar 2019.

Haka kuma Nweze ne ya gabatar da hukuncin da ya bayyana tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Ahmad Lawan a matsayin ɗan takarar Majalissar Dattawa mai Wakiltar Yobe ta Arewa a jam’iyyar APC domin shiga zaɓen da ya gabata.

Justice Nweze dai ɗan asalin garin Obollo ne da ke Ƙaramar Hukumar Udenu a Jihar Enugu, kuma an haife shi a ranar 25 ga watan Satumba na shekarar 1958.

A shekarar 2014 gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ta amince da buƙatar Majalissar Shari’a ta Ƙasa na naɗa Nweze a matsayin alƙalin Kotun Ƙoli.

Comments
Loading...