For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

YANZU-YANZU: An Kashe Mutane 28 A Kudancin Kaduna

Rahotanni sun tabbatar da cewa, a jiya Lahadi da dadare, wasu ƴanta’adda sun kashe mutane sama da 28 a hare-hare mabanbanta da suka kaiwa al’ummomin Malagum 1 da Sokwong a yankin Kagoro da ke Karamar Hukumar Kaura da ke jihar Kaduna.
Shugaban Karamar Hukumar Kaura, Mathias Siman wanda ya tabbatar wa jaridar PUNCH labarin a yau Litinin ya ce, zai iya tabbatar da mutuwar mutane 7 da aka yi wa kisan gilla a Sokwong.
Wannan harin dai na zuwa ne kwanaki biyar bayan an ƙaddamar da wani harin a Malagum 1, inda mutane uku suka rasa ransu.
Shugaban Karamar Hukumar ya ce ƴanta’addar sun kone dukkanin gidajen da ke Sokwong, amma har yanzu bai tabbatar da mutuwar mutane a Malagum 1 ba.
Mathias, ya yi kira ga mazauna yankin da su samu natsuwa, yayin da aka samar da jami’an tsaro don su kula da yankin.
Haka kuma, Kakakin Majalissar Kansilolin Karamar Hukumar Kaura, Atuk Stephen ya ce, sama da mutane 22 ne aka tabbatar an kashe a Malagum 1, yayinda aka kashe mutane takwas a Sokwong.
Atuk ya bayyana kisan a matsayin na rashin imani, inda yai kira ga Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro da su ninka kokarinsu domin su yi maganin sabbin kashe-kashen.
Mai magana da yawun Rundunar Ƴansandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige bai samu ba a kokarin da akai na tuntubarsa a lokacin da ake hada wannan rahoton.

Comments
Loading...