For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

YANZU-YANZU: An Yi Garkuwa Da Wasu Mutane 46 A Wani Sabon Hari A Kaduna

Akalla mutane 46 aka yi garkuwa da su a Agunu Dutse, da ke mazabar Agunu ta karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Wani mazaunin wajen da ake kira da Maurice Clement Tanko (Galadiman Agunu Dutse), ya baiyanawa jaridar DAILY TRUST cewa masu garkuwa da mutanen sun shiga yankin ne a aranar Alhamis da misalin karfe 12:30 na dare.

“Da misalin karfe 12:30 na dare ne, ‘yan sakanmu suka gano wani motsi na daban a cikin yankinmu kamar nisan mita 200 da kuma haske-hasken fitila amma babu magana,” in ji shi.

“Sannan yan fashin sun cigaba da kai farmaki har tsawon mintuna 10 zuwa 20, amma sai suka fahimci yan sakai sun samu labari”.

Ya kara da cewa mutum daya daga yankin, Abubakar Sule, ya samu rauni a yayin harin, amma yanzu haka yana ci gaba da karbar kulawa daga likitoci.

Kakakin hakumar ‘yan sanda ASP Muhammad Jalige bai ce kamai ba dangane da lamarin ba.

(DAILY TRUST)

Comments
Loading...