Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’yyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, ya zabi Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin wanda zai mara masa baya a matsayin dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa.
Da yake jawabi ga Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar yau Alhamis a ofishin jam’iyyar da ke Abuja, Atiku ya ce, ya tuntubi dukkanin bangarorin jam’iyyar kafin ya yanke wannan hukunci, inda ya kara da cewa, hadin kan jam’iyyar yana da matukar tasiri wajen yakin neman zabe.
Ya kuma yi kira ga dukkan wadanda aka gabatar da sunayensu domin samun matsayin da su yi aiki tare da shi, inda ya kara da cewa, “Ina farincikin sanar da wanda zai mara min baya. Wannan kuwa shine Ifeanyi Okowa.”
Akwai karin bayani . . .