Shugaban Kasa Muhammadu ya nada Muazu Jaji Sambo dan asalin jihar Taraba a matsayin sabon ministan Najeriya.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa Shugaban Majalissar Dattawa, Ahmad Lawan a ranar Talata, ya karantawa ‘yan majalissar wasikar shugaban kasar kan nadin, tare da kira garesu da su tantance tare da tabbatar da wanda aka nada din.