For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

YANZU-YANZU: Gwamna Fintiri Ya Sanya Dokar Hana Fita A Jihar Adamawa

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya ayyana dokar hana fita ta tsawon awanni 24 a jihar, biyo bayan hare-haren da ƴanbindiga suke kaiwa mutane a babban birnin jihar, Yola.

Gwamnan ya bayyana cewar, dokar ta fara aiki nan take a yau Lahadi, 30 ga watan Yuli, 2023, wanda hakan ke nufi da an hana zirga-zirga a duk faɗin jihar daga safiyar yau.

Sanarwar umarnin gwamnan ta fito ne daga Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Humwashi Wonosikou, a safiyar ta yau Lahadi.

Labari Mai Alaƙa: Ƴan Bindiga Sun Kashe Babban Malami, Manoma 5, Sun Yi Garkuwa Da Mutum 40 A Kaduna

Sanarwar ta ce, iya waɗanda ake da tsananin buƙatar aiyukansu kuma masu shaidar aiki ingantacciya ne kaɗai aka yarda su yi zirga-zirga a lokacin dokar hana fitar.

Gwamna Fintiri ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi biyayya ga dokar, inda ya ƙara da cewa, duk mutumin da aka kama da karya dokar zai fuskanci fushin hukuma.

Comments
Loading...