For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

YANZU-YANZU: Gwamnatin Tarayya Zata Cire Tallafin Mai Bayan Watanni 18 Masu Zuwa

Gwamnatin Tarayya, a yau Talata ta bukaci karin wa’adin watannin 18 kafin tabbatar da cire tallafin mai gaba daya.

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa za ta mika kudirin neman gyaran dokar man fetur ta PIA domin tabbatar da hakan.

Karamin Ministan Albarkatun Mai, Timipre Sylva ne ya sanar da haka yayin da yake jawabi ga manema labarai na Fadar Shugaban Kasa a Abuja.

Ministan ya ce, Gwamnatin Tarayya za ta fuskanci Majalissar Tarayya domin gyaran sabuwar dokar man fetur ta PIA.

Comments
Loading...