Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress, APC, na yankin Arewa sun goyi bayan jam’iyyar ta miƙa takarar Shugaban Ƙasa zuwa yankin Kudu.
Sun yanke wannan hukunci ne a daren yau Asabar, a wani zama da suka yi a Abuja.
Gwamnonin APCn na Arewa, sun kuma buƙaci dukkanin masu neman takarar Shugaban Ƙasa daga yankin Arewa da su janye.
Akwai ƙarin bayani….