Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya rubuta wa Majalissar Dattawa bukatar sake gyara sabuwar dokar zaben da ya sanya wa hannu a Juma’ar da ta gabata.
A wasikar da Shugaban Kasar ya rubuta wadda Shugaban Majalissar Dattawa Ahmad Lawan ya karanta a zaman Majalissar na yau, Shugaban ya bukaci Majalissar da ta duba yiwuwar goge sashi na 84(12) na Dokar Zabe ta 2022.
Sashin dai shine wanda yake magana a kan ajjiye aikin masu rike da mukaman siyasa kafin su shiga sabgar zaben fidda gwani.
Shugaban Kasar ya baiyana sashin a matsayin mai nuna wariya ga masu rike da mukaman siyasa.