Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta saki ƙa’idojin yanda babban zaɓen shekarar 2023 zai gudana.
Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce, da gabatar da dokoki da ƙa’idojin, hukumar ta kammala duk wasu shirye-shirye domin gudanar da zaɓen.
Ya ce, wannan ne karo na farko da hukumar ta taɓa gabatar da ƙa’idojin watanni tara kafin babban zaɓe.
Akwai ƙarin bayani nan gaba….