For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

YANZU-YANZU: Jami’an Tsaro Sun Mamaye Majalissar Jihar Cross River Bayan Hukuncin Kotu

Yansanda dauke da makamai a safiyar Talatar nan sun kwace Majalissar Jihar Cross River.

‘Yansandan da suka fito daga rundunar yaki da garkuwa da mutane da kuma sauran ‘yansanda sun kuma bazu zuwa hanyoyin da ke sadar da mutane da Majalissar Jihar.

Haka kuma, an hana zirga-zirga a yankin Majalissar da ke Dimond Hill.

KARANTA: Kotu Ta Ƙwace Kujerun Ƴan Majalissa 20 Saboda Sauya Sheƙa Zuwa APC

Matakin na ‘yansandan ya biyo bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin din jiya, inda ta kori ‘yan majalissa 20 wadanda suka bar jam’iyyar PDP suka koma jam’iyyar APC.

(PUNCH)

Comments
Loading...