Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar PDP.
Jaridar NIGERIAN TRACKER ta baiyana cewa, Kwankwaso ya baiyana hakan ne a wasiƙar da ya aikewa shugaban PDP na mazaɓarsa.
Tun a farkon watan nan ne tsohon gwamnan ya baiyana aniyarsa ta ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar NNPP kafin ƙarewar wannan watan na Maris.
A ranar Lahadin da ta gabata ne ɗan takarar Gwamnan Jihar Kano ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2019, Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam’iyyar shi ma.