Wani beni mai hawa da dama da ke kan Lagos Street a yankin Garki da ke Abuja ya rushe, inda mutane kusan 37 suka rasa rayukansu wasu kuma da dama suka maƙale a cikin ɓaraguzai, in ji PUNCH.
Lamarin dai ya faru ne a daren jiya Laraba bayan mamakon ruwan sama da aka samu a birnin wanda ya fara da misalin ƙarfe 11 na dare.
Da ta ke tabbatar da faruwar hatsarin, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Tarayya, FEMA ta ce, an samu nasarar ceton mutane 37 waɗanda a cikinsu wasu biyu suka samu manyan raunuka.
KARANTA WANNAN: Jihar Kaduna Ta Fara Gina Babban Birni Mai Gidaje Dubu 500,000 Don Talakawa
Babban Daraktan FEMA, Dr. Abbas Idris, a wata sanarwar gaggawa da ya fitar a safiyar yau Alhamis ya ce, mutane 37 da aka tseratar, an kai su wuraren shan magani daban-daban da ke Abuja, sannan kuma ya ce, har yanzu ana ci gaba da aikin ceto haɗin guiwa da sauran masu bayar da agaji.
Ya ƙara da cewar, yanzu haka, jami’an FEMA na Abuja, da na Hukumar Kiyaye Haɗɗura, da Ƴansandan Babban Birnin Taryya, da VIO na wajen da hatsarin ya faru domin bayar da agaji.
Wani da shaida abun da ya faru, ya bayyana a wani shafin yaɗa labarai na yanar gizo cewar, benin ya ɗauke da ɗakuna da dama, sannan kuma ƙasansa cike ya ke da shaguna.