For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

YANZU-YANZU: Peter Obi Ya Ce Ya Fi Son Zaɓar Mai Ƙarancin Shekaru A Matsayin Mataimaki

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, a yau Laraba ya bayyana ƙudirinsa na zaɓin wanda zai masa mataimaki, inda ya ce, ya fi son mai ƙarancin shekaru ya zame masa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.

Tsohon Gwamnan na Jihar Anambra, Peter Obi, ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise TV a shirinsu na safiyar nan.

Ya ƙara da cewa, ya fi son mai ƙarancin shekaru wanda yake da gudunmawar da zai iya bayarwa ga takararsa maimakon tsofin hannu waɗanda suka taɓa kasancewa a gwamnati kafin yanzu.

Akwai ƙarin bayani nan gaba . . .

Comments
Loading...