Al’ummar Musulmai a Najeriya na jimamin rasuwar sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Gero Argungu wanda ya rasu a asibitin Birnin Kudu a yau Laraba.
Shugaban Ƙungiyar Izala na Ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana a shafinsa na Facebook cewar, Argungu ya rasu ne bayan jinya da yayi na ɗan lokaci a Birnin Kebbi.
Ya sanar da cewar, za a masa sallar janaza gobe Alhamis a lokacin da za a sanar nan gaba a garinsu Argungu da ke Jihar Kebbi.