Wata yarinya mai shekaru 14 da haihuwa ‘yar kasar Faransa mai suna Fatima Musa ta bar tarihi a makarantar Nurul Tilawah International School, Zaria, Jihar Kaduna, inda ta haddace Al-Kur’ani Mai Girma cikin watanni hudu kacal.
Abu ne da aka saba, a samu haddar Al-Kur’ani cikin shekara guda musamman ga kananan yara, amma cikin watanni hudu kacal wannan abun mamaki ne babba.
Fatima wadda ta kasance ‘yar Musulmai a kasar Faransa ta zo Najeriya ne tare da yayarta,
Anijou Musa domin koyon ilimin addinin Musulunci.
Makarantar da suka zo tana unguwar Gonar Ganye a Zaria, kuma makarantar ta saba karbar dalibai daga kasashen Afirka da na Turai tsawon sama da shekaru 25 da suka wuce.
Mai Makarantar wani tsohon Mai Bayar da Shawara ne ga tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a kan harkokin Babban Masallacin Abuja wanda ake kira da Tahir Umar Tahir.
Daraktan makarantar, Nura Umar Tahir ya ce, makarantar ba ta taba samun irin wannan kokari ba a cikin dalibanta tun bayan fara makarantar.
Ya bayyana cewa, Fatima tana haddace shafuka 6 ne a sati a farkon lokacin da aka sa ta a makarantar a watan Satumba na shekarar 2021, inda daga baya take haddace shafi 8 a duk rana sabanin shafuka 2 zuwa 3 da sauran dalibai suka saba haddacewa.
Daraktan ya ce, “Fatima yarinya ce ta musamman, wadda duk da ba ta da surutu amma tana da yawan tambaya da kuma kula sosai, ko yaushe tana cikin neman ilimi.
“Tana jin dadin yin tambaya a kai a kai, kuma idan ta yi tambaya, tambayar ta kan zama babba wadda ta fi karfin ‘yan shekarunta,” in ji Daraktan.