Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa sama da yara 300,000 ne suka rasa rayukansu a cikin shekaru 12 da suka gabata saboda rikicin da ya addabi yankin Arewa maso Gabas.
A sabuwar kididdigar da ta fitar, UNICEF ta bayyana cewa sama da mutane miliyan daya ne suka rasa muhallansu a cikin lokacin.
Hukumar ta kara bayyana cewa akalla yara 5,129 da ba sa zuwa makaranta ne a halin yanzu suke fama da matsalolin tabin hankali sakamakon rikicin.
A cewar wata sanarwar hadin gwiwa da Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da UNICEF suka fitar, sun ce wani shirin kiwon lafiya na Mental Health and Psychosocial Support (MHPSS) na bukatar tantance yaran da rikicin ya shafa a Arewa Maso Gabashin Najeriya; ya bayyana wahalar rayuwa da a ke ganewa ta damuwa, tuhuma, fushi, tashin hankali, da tsananin tsoron da yaran ke ciki.
Wakilin UNICEF a Najeriya Peter Hawkins ya ce “tabon rikice-rikicen gaskiya ne kuma yana dawwama a jikin yaran.”
“Yara da yawa a Arewa Maso Gabashin Najeriya suna fadawa rikicin da ba ruwansu a ciki. Dole ne a daina hare-hare kan yaran cikin sauri. A halin da ake ciki, mun kuduri aniyar yin aiki tare da abokan huldar mu don samar da ilimin halayyar dan adam da sauran tallafi ga yaran da rikicin ya shafa domin su dawo hayyacinsu su kuma sake samun rayuwa.”
An danganta rashin kaifin hankalin yaran da bacin ran da suke shiga. Yaran da rikicin ya shafa suna cikin hadarin lafiyar hankali na tsawon lokaci da al’amuran rashin daidaito.
Yayin da yaran ke ci gaba da kasdancewa cikin burbushin rikicin shekaru 12 a Arewa Maso Gabashin Najeriyar, kungiyar EU da UNICEF na aiki tare don samar da ayyukan jin kai da nufin inganta lafiyar hankalin yara.
Da tallafin EU da na UNICEF don temakawa wajen farfadowar yaran, akalla yara 5,129 wadanda ba sa zuwa makaranta a jihar Borno, cikin kananan hukumomi shida suna samun ayyukan jin kai, ciki har da tallafi domin samun lafiyar kwakwalwa da walwala don karfafa jin dadi, juriya, kwarewa, da dogaro da kai.
Har ila yau, aikin yana tallafawa yara masu rauni a duk fadin jihar Borno tare da ba su kariyar matsalolin kiwon lafiya, da samar musu da kwarewa a fannin ilimi, da kuma samar musu adalci da tsaro.
Duk wadannan ana yin su a karkashin taimakon jin kai wanda ya zuwa yanzu ya baiwa yara 15,552 wadanda ba sa zuwa makaranta horo. Ya kuma samawa yara 1,610 da ba sa zuwa makaranta kwarewa a karatu da rubutu da kuma yara 5,194 da suka shiga cikin makarantun Alkur’ani a duk fadin kananan hukumomin jihar.
A cewar Shugaban Hadin Kan Tarayyar Turai Cecile Tassin-Pelzer, “Samar da jin dadin rayuwa da habaka yara da malamai bangare ne na sake samar da ilimi da kuma ba da damar yara su sake shiga makarantu lafiya.”
Shirin da EU ke bayarwa a jihar Borno wani bangare ne na kunshin tallafin Tarayyar Turai na kudi Euro miliyan 10 don farfado da yaran da tallafawa matasa, da al’ummomin jihar Borno.
Har ila yau a cikin kunshin akwai koyar da sana’o’i da kuma ilimin mu’amalar yau da kullum ga matasa akalla 25,000, da kuma ginawa da gyara cibiyoyin koyo, da karfafa tsarin bayanan ilimi.