For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Yau Sabbin Ministocin Tinubu Zasu Fara Fuskantar Tantancewar Majalissar Dattawa

A yau Litinin ne Majalissar Dattawa zata fara tantance ingancin waɗanda Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ke son naɗawa ministoci.

A ranar Alhamis da ta gabata ne, Shugaban Majalissar Dattawa ya karanta sunayen mutane ashirin da takwas da Tinubu yake son naɗawa ministoci ga majalissar, inda aka ɗage duk wani aikin majalissar da nufin fara tantance ministocin a yau Litinin.

Mai Magana da Yawun Majalissar Dattawa, Sanata Mai Wakiltar Ekiti ta Kudu, Yemi Adaramodu ya ce, ba zasu ƙayyadewa kowanne minista lokacin da zai ɗebe a gaban majalissar yana magana ba.

Ya ƙara da cewa, a ranar farko yau Litinin zasu fara tantancewar da misalin ƙarfe 11 na safe, yayinda sauran ranakun zasu na farawa da misalin ƙarfe 10 na safe. Ta ce, zasu saurari waɗanda ake son naɗawar sosai kan tanade-tanadensu wajen ciyar da ƙasa gaba, inda ya ce dukkan ƴan Najeriya ma zasu iya shaida tantancewar.

Comments
Loading...