For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Yawan Wadanda Ke Rayuwa Cikin Talauci A Najeriya Zai Kai Miliyan 95.1 A 2022 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya ce, rage radadin fatara a Najeriya ya tsaya cik tun a shekarar 2015, inda ‘yan Najeriya da dama suka fada cikin kangin talauci na tsawon shekaru.

An dai zabi Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, a matsayin shugaban Najeriya a shekarar 2015.

A cewar bankin da ke birnin Washington, ana hasashen adadin talakawan Najeriya zai kai miliyan 95.1 a shekarar nan ta 2022.

Talaucin dai na nufin rashin samun zarafin yin rayuwa a rana guda a kan kudin da ya kai dala 1.9, kwatankwacin naira 1000 a halin yanzu.

Bankin ya bayyana hakan ne a cikin rahotonsa mai taken, ‘Kyakkyawar Makoma ga Daukacin ‘yan Najeriya: Binciken Matsayin Talauci a Najeriya Na 2022’.

Rahoton ya ce a wani bangare, “Raguwar Talauci ta tsaya cak tun 2015.”

Ya kara da cewa, “A bisa ga dukkan alamu raguwar talauci a Najeriya ta tsaya cik a cikin shekaru goma da suka gabata, bisa ga dabaru na kisa na baya-baya da bincike-bincike. Ƙididdiga mafi kyau daga tsarin da aka yi na baya-bayan nan ta nuna cewa yawan talauci – a layin talauci na duniya – ya kasance kashi 42.8 cikin 100 a shekarar 2010.

Bankin ya kuma nuna cewar abubuwan sun ta kara kamari musamman saboda saurin karuwar al’ummar Najeriya.

Tsananin matsin tattalin arziki da aka samu a shekarar 2016 da kuma annobar Korona na a kan gaba wajen kar tsunduma Najeriya cikin matsanancin talaucin, inda ya ce, cutar ta Korona ta jefa sama da ‘yan Najeriya miliyan biyar cikin talauci nan da shekarar 2022.

Rahoton ya ce kimanin ‘yan Najeriya miliyan 90 ne ake sa ran za su kasance matalauta a shekara ta 2022, yayin da kuma dalilin sakamakon annobar ta Korona, hasashen ya karu zuwa ‘yan Najeriya miliyan 95.1.

Comments
Loading...