Ƙungiyar Yiaga Africa ta ke rajin bunƙasa demokaraɗiyya, ƴancin ɗan’adam da damawa da al’umma, ta yi kira da a soke amfani da katin zaɓe, PVC a matsayin hanya ɗaya tilo ta samun damar kaɗa ƙuri’a a zaɓukan Najeriya.
Shugaban Gudanarwa na Ƙungiyar, Dr. Hussaini Abdu ne yai wannan kiran jiya Juma’a a Abuja, lokacin gabatar da rahoton ƙungiyar kan Zaɓen Najeriya na 2023.
Labari Mai Alaƙa: El-Rufa’i Zai Haɗa Faɗa Tsakanin Tinubu Da Shettima – Shehu Sani
Dr. Hussaini Abdu ya ce, yarda da ɗaukar wannan matakin zai temaka wajen magance matsalolin da ake fuskanta na rashin karɓar katin zaɓe da kuma tantance masu kaɗa ƙuri’a abubuwan da kan daƙile ƴancin masu kaɗa ƙuri’a da dama.
Ya jaddada cewar akwai buƙatar a sake duba ƙa’idojin da ake sanyawa masu son kaɗa ƙuri’a, musamman saboda shigowar BVAS da ke ajjiye bayanan hotunan yatsun masu kaɗa ƙuri’a.
Ya buƙaci Majalissar Tarayya da ta gyara dokar zaɓe yanda Hukumar INEC zata sami damar fitar da waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri’a daga kundin bayanan Hukumar Kula da Rijistar Ɗan Ƙasa, NIMC, abin da ya ce zai jawo rage kashe kuɗaɗe yayin shiryawa zaɓe.
