
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta ce, Dokar Zabe ta Shekarar 2022 ta bayar da damar cin tarar kudi naira dubu dari biyar (₦500,000) ko daurin shekara daya a gidan yari ko kuma gaba daya, ga duk wanda aka kama da laifin sayan kuri’u a lokacin zabukan 2023.
Kwamishinan hukumar na Jihar Jigawa, Farfesa Muhammad Lawal Bashar ne ya bayyana hakan ta cikin wani shiri na musamman na Radio Jigawa.
Kwamishinan ya ce tuni hukumar INEC ta shirya domin gudanar da zabe da na’urar BVAS wadda za ai amfani da ita wajen tantance masu zabe domin kada kuri’a, inda wanda ya yi rijistar fiye da sau daya ba zai samu damar kada kuri’a ba.
Farfesa Muhammad Lawal ya ce, hukumar zabe a Jihar Jigawa ta karbi katinan zabe na dindin din sama da dubu dari da hamsin da shida, wanda ya zuwa yanzu ake cigaba da rabawa a kananan hukumomi da kuma mazabu har zuwa ranar 22 ga watan Janairu, 2023.
Ya shawarci wadanda suka yi rijista da su hanzarta karbar katinan nasu domin samun damar kada kuri’a a zabukan dake tafe.
Kwamishina ya kara da cewa hukumar ta yi kyakkyawan tsari da zai baiwa masu bukata ta musamman da tsofaffi da kuma mata masu juna biyu damar kada kuri’a cikin sauki.
Da ya juya ga batun jami’an tsaro kuwa, ya ce a wannan karon doka ta bayar da damar cewa dukkan jami’an tsaron da zasu gudanar da aikin zabe sai an rantsar da su.