Ministan Sadarwa daBunkasa Tattalin Arzikin Sadarwa, Dr. Isa Ali Pantami, ya ce za a fara anfani da Network mai karfin 5G a Najeriya a watan Janairun 2022.
Ministan ya ce hakan zai taimaka matuka wajen sa ido kan barnatar da dukiyoyin jama’a.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Maiduguri a wajen wani babban taro domin magance barnata wutar lantarki da kayayyakin sadarwa.
Rahotanni sun nuna cewa, taron wanda Ma’aikatar Yada Labarai da Al’adu ta shirya, ya samu halartar gwamna Babagana Zulum na Borno da mataimakinsa, Mista Usman Kadafur da sauran masu ruwa da tsaki.
Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya jagoranci sauran ministocin wadanda suka kasance jagorori a taron.
Pantami, wanda Mista Ubale Maska, Kwamishina a ma’aikatar Sadarwa ta Najeriya ya wakilta, ya ce kwanan nan Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da hanyar sadarwa ta 5G don habaka sadarwa a kasar.
Ya ce yayin da fasahar za ta inganta sa ido kan masu aikata laifuka da ke lalata kayayyakin jama’a a duk fadin kasar, ya kamata a sanya wasu matakan da za ai amfani da su wajen kamo su tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Ministan ya bayyana cewa akwai cibiyoyin sadarwa sama da 50,000 a duk fadin kasar nan, wadanda zai wahala ga mutum da hannu ya bibiye sub a tare da fasahar zamani ba.
Ya kuma bayyana cewa an samu katsewa kusan 16,000 ta hanyoyin sadarwa a bangarorin kamfanonin sadarwa na MTN, Globacom, Airtel da 9Mobile daga Janairu 2021 zuwa Yuli 2021.
Katsewar, a cewarsa ta faru ne saboda katsewar wayar fiber, hana damar shiga da kuma sata wanda ke haifar da lalacewar sabis a yankunan da abin ya shafa.