Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalissar Koli ta Addinin Musulunci, Sa’ad Abubakar, ya umarci Musulmi da su fara duban jaririn watan Sha’aban, wata na 8 a jerin watannin Musulunci a yau Alhamis 3 ga watan Maris, 2022.
Sarkin ya bayar da wannan umarnin ne a wata sanarwa da Shugaban Sashin Bayar da Shawarwari kan Al’amuran Addini na Masarautar Sarkin, Sambo Junaidu ya sanya wa hannu a jiya Laraba.
“Ana sanar da al’ummar Musulmi cewa, ranar Alhamis, 3 ga watan Maris, 2022 wadda tai dai-dai da 29 ga watan Rajab, 1443, rana ce da tai dai-dai da ranar fara duban jaririn watan Sha’aban, 1443.
“Saboda haka, ana bukatar Musulmi da su fara duban sabon watan a ranar Alhamis tare da sanar da ganinsa ga digaci/bulama mafi kusa da su domin a sanar da Mai Alfarma Sarkin Musulmi.
Watan Sha’aban dai shine wata na 8 a jerin watannin Musulunci wanda kuma shi ne na karshe da ke zuwa kafin watan Azumin Ramadhan wanda Musulmi a fadin duniya suke matukar girmamawa.
Idan har an samu ganin watan na Sha’aban a yau Alhamis, Musulmi za su iya fara azumi a ranar Asabar 2 ga watan Afrilu na shekarar 2022, kimanin nan da kwanaki 30 masu zuwa kenan.
(NAN)