Kudin Turkiyya wato Lira na ci gaba da faduwa a kasuwar canji ta duniya inda ta kara faduwa da kashi 6 cikin 100 a daidai lokacin da ake cikin fargabar hauhawar farashin kayayyaki a kasar.
Wannan na zuwa ne bayan rage adadin kudin ruwa a kasar a ranar Alhamis.
Shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan ya kuma sanar da cewa zai kara mafi karancin albashin kasar da kashi 50 cikin 100 inda ake kyautata zaton idan aka yi hakan farashin kayayyaki zai karu.
Erdogan ya dage kan cewa zai iya dakile hauhawar farashin kayayyaki duk da rage kudin ruwan da ya yi, sai dai yan kasuwa na cikin fargaba.
A bana kadai, sai da darajar kudin ta ragu da kashi 50 cikin 100, inda aka fi samun raguwar a watan da ya gabata.
Daga: BBC Hausa