For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Za A Rataye Matashiyar Da Ta Kashe Makwabciyarta A Kano

Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Miller Road ta yanke wa wata matsashiya hukuncin kisa ta hanayar rataya bisa laifin kashe makwabciyarta.

Ana zargin matashiyar ne dai da laifin kashe makwabciyarsu mai suna Bahijja da wuka bayan ta kira ta karuwa.

Alkaliyar kotun, Mai Shari’a Amina Adamu, ta ce ta same ta da laifin kisan kai ne bayan samun gamsassun hujjoji, abin da ya sa wadda aka yanke wa hukuncin fashewa da kuka.

Bayan kammala shari’ar ne lauyan gwamnati cikin barkwanci ya bayyana wa manema labarai cewa kamata ya yi a hada aurenta da wani dan Hisba da shi ma aka yanke wa hukuncin kisa, sakamakon kashe bazawararsa.

AMINIYA

Comments
Loading...