Wata Babbar Kotu a jihar Kano, ta yankewa wani mutum mai suna Aminu Inuwa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunsa da laifin kasha matarsa, Safara’u Mamman.
Inuwa, wanda ke zaune a yankin Gwazaye na unguwar Dorayi Babba a Kano ya samu wannan hukunci ne a Talatar nan.
Alkali Usman Na’abba, wanda ya tabbatar da hukuncin, ya bayyana cewa masu gabatar da karar sun gabatar da karfafan hujjojin da suka tabbatar da laifin Inuwa.
Tun da farko, mai shigar da karar, Lamido Sorondinki ya sanar da kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 2 ga watan Afrilu na shekarar 2019 a yankin Gwazaye na unguwar Dorayi Babba.
Ya kara da cewa, “wanda ake zargin ya yanka makogwaron matarsa ne da wukar aikin gida lokacin da husuma ta shiga tsakaninsu.
“Daga baya Inuwan ya binne matar tasa bayan ta mutum a cikin wani daki da ba a kammala a gidansa da ke Dorayi Babba.”
Mai shigar da karar ya gabatar da shaidu 3 da kuma hujjoji 6 domin tabbatar da laifin wanda ake zargin.
Sai dai kuma wanda ake zargin ya musa cewa ya aikata laifin.
Lauyan wanda ake zargin, Mustapha Idris, ya iya gabatar da shaida guda daya ne don kare wanda yake karewa.
(NAN)