For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Za A Siyar Da Litar Fetur Ƙasa Da Naira 200 Idan Matatun Mai Na Aiki

Shugaban Ƙungiyar Dillalai Man Fetur Masu Zaman Kansu ta Najeriya, IPMAN, reshen Jihar Rivers, Joseph Obele, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar da cewar an gyara matatun man Najeriya kamar yanda aka tsara.

Ya ce, farashin man fetur zai sauƙo ƙasa da naira 200 a duk lita ɗaya idan har aka ce matatun man na aiki.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake fama da wahalhalun da janye tallafin man fetur ya jawo wa ƴan ƙasa, da suka haɗa da tashin gwauron zabbin da farashin man ya yi da kuma tsadar rayuwa da ya far.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Rufe Filin Jirgin Sama Na Lagos

Domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin cewar Matatar Mai ta Port Harcourt za ta fara aiki a watan Disamba na wannan shekara.

A jiya Juma’a, Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur Ɓangaren Mai, Sanata Heineken Lokpobiri, a wata ziyara da ya kai Matatar Mai ta Port Harcourt, ya jaddada shirin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da tayar da matatar.

Shugaban IPMAN na Jihar Rivers ɗin ya ƙara da cewar, ƙarancin dala na ci gaba da zama matsala ga masu shigo da mai, inda ya ce, farashin man zai ci gaba da tashi matuƙar gwamnati ta gaza samar da mafita da wurwuri.

Comments
Loading...