For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Za A Tantance ‘Yan Takarar Shugabancin APC A Kano Kan Amfani Da Miyagun Kwayoyi

Dukkanin ‘yan takarkarun neman shugabancin jam’iyyar APC a jihar Kano za su fuskanci tantancewa kan ko suna ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Kwamishinan Yada Labarai na jihar Kano, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a shirye-shiryen babbataron jam’iyyar APC na jihar wanda za a gudanar ranar 16 ga Oktoba.

Ya umarci ‘yan takarkarun da su ziyarci ofishin Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) na Kano daga karfe 7 na safiyar ranar Talata.

Ya kuma yi gargadin cewa babu wani dan takara da za a bari yai takara idan bai je an masa gwajin ba.

Kwamishinan ya bayyana cewa, wannan na cikin yunkurin gwamnatin jihar Kano na kawar da dukkan wani nau’i na ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.

Ya bayyana cewa a lokacin zaben kananan hukumomin da ya gabata a jihar ma, an gudanar da irin wannan gwaji ga ‘yan takarkarun da suka nemi shugabancin kananan hukumomin, haka kuma an gudanar da hakan wajen nadin masu rike da mukaman siyasa da suka hada da ‘yan majalissar zartarwa kafin a amince da su.

A lokacin binciken ‘yan takarkaru na majalissun kananan hukumomin da aka gudanar, an sami ‘yan takarar kansila guda 13 da lefin ta’ammali da kwayoyin kuma an hana su takara.

Kwamishinan ya kara da cewa, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya riga ya sanar da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA maganar za su gudanar da gwajin.

Comments
Loading...