For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Za A Yanke Hukunci Kan Karba -Karba A Lokacin Da Ya Dace – PDP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da kungiyar gwamnoninta a ranar Asabar sun ce jam’iyyar za ta yanke shawarar inda za ta karkatar da mukaman siyasa a lokacin da ya dace kafin babban taron jam’iyyar, wanda za a yi ranar 30 ga watan Oktoba.

Jam’iyyar da kungiyar gwamnoninta sun bayyana hakan a cikin wasu kalamai da aka fitar a Abuja a ranar Asabar don mayar da martani ga Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi kan sharhin batun karba -karba na shugabanci da ya yi gabanin babban taron jam’iyyar na kasa.

Umahi ya zargi PDP da cewa ba a shirye ta ke ba wajen bayar da tikitin takarar shugaban kasa na 2023 zuwa yankin Kudu.

Kungiyar Gwamnonin PDP, a cikin wata sanarwa da Babban Daraktanta, Hon. C.I.D Maduabum ya fitar, ya ce kungiyar ta fusata da Umahi, wanda ya bar PDP zuwa All Progressives Congress (APC), yana kokarin “yin karya a kanta”.

Maduabum ya shawarci Umahi, wanda ya yi zargin ya yiwa PDP zagon kasa a zaben shugaban kasa na 2019 a jihar, da ya mai da hankali kan rawar da yake takawa a APC ya bar PDP ita kadai.

Dangane da batun karba-karba, Maduabum ya shawarci Umahi da ya fuskanci matsalolin sa a cikin APC kuma kada ya ja PDP da Gwamnoninta cikin matsalolin.

“Jam’iyyar PDP jam’iyya ce mai zaman kanta wacce ke da tsarin aiki da hanyar yin abubuwa. Ba bangare bane na APC ko kuma na wata ƙungiya.

“Jam’iyyar PDP za ta yanke hukunci kan batun raba ofisoshin siyasa a lokacin da ya dace. Ko itama APC har yanzu ba ta yanke shawara kan batun karba -karbar ba.

“Kungiyoyi da ra’ayoyi daban -daban suna cigaba da muhawara don kare matsayinsu kamar yadda ake bukata a dimokuradiyya. A karshen lamarin, kowane bangare na siyasa zai yanke hukunci.”

Maduabum ya ce PDP ta yi niyya kan kudirin ta na karbe mulki daga hannun APC a 2023 kuma za ta yi dabarun cimma wannan don maslahar kasa da ci gaban dimokuradiyyar Najeriya.

A wata sanarwa ta daban, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa, Mista Kola Ologbondiyan, ya bukaci Umahi ya mai da hankali kan jam’iyyarsa ta APC ya bar PDP ita kadai.

Ologbondiyan ya ce ya kamata Umahi ya sani cewa PDP jam’iyya ce me bin doka da oda kuma duk masu ruwa da tsaki da ke cikin PDP za su yanke hukunci cikin kwanciyar hankali idan lokaci ya yi.

Ya ce Umahi na son gabatar da ajandarsa ta karba -karba a APC amma ba zai yi hakan ba saboda ya san ‘yan Najeriya za su shiga PDP a 2023.

A ranar Juma’a Umahi ya yi wa Kungiyar Gwamnonin PDP izgili kan kudirin da Kungiyar Gwamnonin Kudu da suka amince da shi na mayar da Mulki zuwa Kudu, yana mai cewa alamu na nuna cewa jam’iyyar PDP ba za ta ba da kujerar Shugaban kasa zuwa Kudun ba.

Gwamnonin Kudun, karkashin jagorancin Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, a cikin wata sanarwar da suka fitar a karshen taron su a jihar Enugu a ranar Alhamis sun tabbatar da matsayarsu kan mayar da mulki zuwa yankinsu.

Umahi, wanda ya yi magana a wani shirin talabijin a ranar Juma’a, ya yi zargin cewa gwamnonin PDP a taron da aka yi a Enugu ba su da gaskiya kan ikirarin da suke yi na son shugabancin Najeriya a 2023 ya koma Kudu.

(NAN)

Comments
Loading...