For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Za A Yanke Hukuncin Kisa Ga Masu Fyade A Jigawa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce duk wanda aka kama da laifin aikata fyade ga yarinyar da ke kasa da shekaru 10 za a yanke masa hukuncin kisa.

Gwamnatin jihar ta ce ta amince da hukuncin kisan ne a kan wadanda suke cin zarafin kananan yara wadanda shekarunsu ba su kai goma ba kamar yanda yake kunshe a Dokar Hakkokin Yara.

Dokar ta ce, duk wanda aka kama da ya yi lalata da yarinyar da kasa da shekaru 10, to za a yanke masa hukuncin kisa.

Kwamishinan Shari’a na jihar Jigawa, Dr. Musa Adamu Aliyu ne ya bayyana hakan a lokacin ganawa da ‘yan jarida a Dutse.

Ya fadawa ‘yan jaridar cewa, duk wanda aka samu da aikata laifin zai fuskanci fushin hukuma ba tare da bashi zabi ko yi masa alfarma.

A shekarar da ta gabata ne, Gwamnan jihar, Alhaji Badaru Abubakar ya sanyawa dokar ta hana ire-iren wadannan laifuffuka hannu, wadanda suka hada da hukuncin kisa da kuma hukuncin daurin rai da rai.

A yanzu haka jihar tana da kararraki 196 a kotuna, yayin da aka tura kararraki 178 neman shawarwarin shari’a.

Kwamishinan ya bayyana cewa, Ma’aikatar Shari’a ta Jigawa tana da kararraki 25 a kotun daukaka kara a Kano, sannan kuma ta kammala manya-manyan kararraki guda 83 manyan kotunan da ke Dutse, Gumel, Kazaure da kuma Ringim.

Kwamishinan ya koka game da matsalar jinkirin kararraki, inda ya ce wannan ne babban kalubalen da ma’aikatarsa ke fuskanta.

Comments
Loading...