Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai rarraba kudi kimanin Dala Biliyan 10 a matsayin wani mataki na farfado da tattalin arziki a cikin kwanakinsa 100 na farko idan ya ci zaben shekarar 2023.
Atiku ya ce, zai yi hakan ne domin ya tallafi masana’antu masu zaman kansu, zai kuma fifita tallafin a bangaren noma, samar da kayayyaki da matsakaita da kuma kananan ‘yan kasuwa.
Atiku ya bayyana hakan ne a wani rubutu da yai a shafin sa da zumunta a jiya Talata da yamma, biyo bayan jawabinsa a Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Lagos, LCCI.
Atiku ya ce, “A kwanaki 100 na farko a matsayin shugaban kasa, zan kirkiri tsarin kudin tallafawa tattalin arziki da nufin sanya hannun jari na kusan Dala Biliyan 10 domin bunkasa matsakaita da kananan ‘yan kasuwa a dukkan bangarorin tattalin arziki.”
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa ya ce, domin Najeriya ta ciyar da tattalin arzikinta gaba, “Fitar da kayan da ba dangin mai ba zai samo mata kudin shiga daga kasashen waje, ya habbaka asusun ajjiyarmu, ya kuma tallafa wajen samarwa Naira daraja. Dukkan wadannan zasu temakawa ci gaban tattalin arziki.”
Ya kuma kara da cewa, “Rage talauci ya kamata ya zama abun da za a baiwa muhimmanci wajen tsarin ciyar da tattalin arzikinmu gaba, haka kuma, ci gaban tattalin arziki ya kamata a gwada shi ta hanyar yawan aiyuka da aka kirkira da kuma yawan mutanen da aka cire daga talauci.
“A karshe, mai da hankali a bangaren da ba sai an ciyo bashi ba ta hanyar bunkasa kamfanonin samar da ababan more rayuwa domin su samar da kudade su kuma samar da manyan ababan more rayuwa.”