A lokacin da yakin neman zaben shugaban kasa na shekarar 2023 ke kara kuratowa, wasu kwararan dalilai na nuni da cewa, gwamnoni hudu na jam’iyyar PDP na yin aiki domin ganin nasarar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu a zaben mai zuwa.
Wata majiya mai karfi ta sanar da DAILYPOST cewa, gwamnoni hudu na Kudancin Najeriya, biyu daga Kudu maso Gabas, dai-dai daga Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu na yin aiki domin tabbatar da nasarar takarar Tinubu.
Majiyar da ta bukaci a boye sunanta ta ce, komai yanzu biyan bukatar kai ne, inda ta kara da cewa, yayin da gwamna daya daga cikin hudun ke neman a tazarce, sauran ukun na neman su kammala su sauka lafiya ne.
Idan za a iya tunawa, jam’iyyar Adawa ta PDP ta bar takarar shugabancin kasa a bude ga kowanne yanki, duk kiraye-kirayen da wasu ‘yan jam’iyyar suka yi na cewa a mika takarar ga bangaren Kudu kadai.
Wannan ne ya baiwa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar damar lashe zaben fidda gwani na neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP domin shiga zaben 2023.
Tun bayan samun nasarar Atikun ne dai, Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike wanda ya zo na biyu a zaben bayan Atiku ke ta jan zare da shugabancin jam’iyyar na kasa da kuma dan takarar.
Gwamna Wike wanda ya alakanta faduwarsa a zaben fidda gwanin da addini da kuma cin amanar da shugabancin jam’iyyar suka yi, musamman ma shugaban jam’iyyar, Dr. Iyorchia Ayu, da kuma Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal wanda janyewarsa daga takarar ya baiwa Atikun nasara abun da Wike ya zarga da yin taron dangi a kansa.