For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zaben 2023: Gwamnonin Arewa Sun Kalubalanci Karba-Karba A Mulkin Najeriya

Gwamnonin yankin Arewacin Najeriya sun kushe matsayar gwamnonin yankin Kudancin kasa na cewar mulki ya koma Kudu a shekarar 2023.

Gwamnonin sun ce, hakan ya saba da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya.

Sun bayyana matsayar ta su ne a zaman da suka gabatar a Litinin a Kaduna.

Shugaban kungiyar, Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ne ya ba da rahoton bayan taron.

Lalong ya ce; “wasu daga cikin gwamnonin Arewan sun nuna goyon baya ga fitar da shugaban kasa na gaba daga yankin Kudu saboda neman hadin kai da zaman lafiya.

“Sai dai kuma, kungiyar gwamnonin dukkansu sun kushe kiran gwamnonin Kudu na cewa dole ne shugabancin kasa ya koma bangarensu na Kudu.

“Maganar ta su ta saba da tanadin tsarin mulki na 1999 wanda akaiwa kwaskwarima, wanda ya ce zababben shugaban kasa dole:- ya samu kuri’u mafiya rinjaye, ya samu kaso 25% na kuri’un da aka kada a kaso 2 cikin 3 na jihohin Najeriya.

Comments
Loading...