For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zaben 2023: INEC Ta Soke Sabbin Katin Zabe Na Mutane Miliyan 1 Da Dubu 100

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta soke sunayen mutane miliyan 1 da dubu 100 wadanda suka yi sabuwar rijistar zabe gabanin babban zaben 2023.

Kwamishinan Hukumar INEC na Kasa kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kan Masu Zabe, Festus Okoye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a yau Talata.

“Kamar yanda ‘yan Najeriya suka sani, ana ci gaba da tantance rijistar katin masu zabe ta amfani da tsarin tantancewa na Automated Biometric Identification System (ABIS) tun lokacin da aka dakatar da ci gaba da yin rijistar a ranar 31 ga Yulin wannan shekara.

“Tun a baya, Hukumar ta sanar da ‘yan Najeriya cewa, cikin sabbin masu rijista miliyan 2,523,458 da suka yi rijista a tsakanin ranar 28 ga watan Yuni na 2021 da 14 ga watan Janairu na 2022, bayanan mutane miliyan 1,126,359 an gano ba su da inganci saboda haka an cire su.”

Ya yi bayanin cewa, tsarin bincike na ABIS a ranar 15 ga watan Janairu zuwa ranar 31 ga watan Yuli na 2022 ya kusa kammala, inda ya bayyana cewa “an gano maimaici na rijista da kuma rashin cancantar wasu inda nan take aka cire sunayensu.

“Irin wadannan sun hada da shigarwa da bayanan da akai wadanda suka saba ka’idar Hukumar. Hukumar ta dau wannan da matukar muhimmanci domin tabbatar da ingantacciyar rijista wadda zata samar da ingantaccen zabe.”

Ya kara da cewa, INEC zata bayyana rijistar masu zaben lokacin da aka kammala tantancewar.

“Bayan haka, za a kara ingantattun masu zaben a kan rijistar da ake da ita ta kasa kafin a saki sunayen a kasa domin tantancewa da kuma karbar korafi daga ‘yan kasa kamar yanda sashi na 19 (1) na Dokar Zabe ta 2022 ya tanada,” in ji wakilin na INEC.

“Muna kara tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa, cikakken bincike yana gudana domin a tsaftace rijistar. Haka kuma, Katin Zabe na Dindindin na duk wadanda suka cancanta za a karbe shi zuwa nan da karshen watan Oktoba da farkon watan Nuwamba kamar yanda akai alkawari.”

Comments
Loading...