Shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a jiya Laraba ya sanar da cewa kundin rijistar masu zabe ya bunkasa zuwa masu rijista miliyan 93.5.
Bayanan farko na rijistar ya nuna cewa, Jihohin Lagos, Kano, Kaduna, Rivers, Katsina da Oyo sune ke da mafi yawan masu rijistar kada kuri’a.
Bayanan sun nuna cewa, Jihar Lagos da kaso 7.57% na masu kada kuri’ar; Kano na da kaso 6.34%; Kaduna na da kaso 4.65%; Rivers na da kaso 3.77%; Katsina da kaso 3.76% da kuma Oyo me kaso 3.51% na masu kada kuri’ar.
Kididdiga ta nuna cewa, masu kada kuri’a a jihohi shidan sun kai mutum miliyan 27.68 wato kaso 29.59 kenan na yawan masu kada kuri’ar a Najeriya.
Kididdigar dai ta nuna cewa, yankin Arewa maso Yamma ne ya fi kowanne yanki yawan masu kada kuri’a, a inda yake da masu kada kuri’a miliyan 22.27.
Sai yankin Kudu maso Yamma wanda yake da masu kada kuri’a mutum miliyan 17.93.
Yankin da ya zo na uku a yawan masu kada kuri’ar shine yankin Kudu maso Kudu mai jihohin Akwa-Ibom, Rivers, Cross-River, Bayelsa, Edo da Delta, inda yake da masu kada kuri’a mutum miliyan 14.4.
Yankin Arewa ta Tsakiya wanda ya hada jihohin Nasarawa, Kogi, Benue, Niger, Kwara, da Plateau yanzu haka yana masu kada kuri’a mutum miliyan 13.8.
Sai yankin Arewa maso Gabas wanda ya hada jihohin Yobe, Borno, Taraba, Adamawa, Bauchi da Gombe a yanzu haka yana da masu kada kuri’a mutum miliyan 12.5.
Sai kuma yankin Kudu maso Gabas da ke kunshe da jihohin Ebonyi, Enugu, Abia, Anambra da Imo yanzu haka yana da masu kada kuri’a mutum miliyan 10.9.
Sai kuma Babban Birnin Tarayya Abuja wanda a yanzu adadin masu kada kuri’ar ya kai mutum miliyan 1.5.
Wannan kididdiga dai ta nuna cewa a cikin manyan yankuna biyu da Najeriya ke da su, Yankin Arewa shine ke ci gaba da kasancewa yanki mai mafi yawan masu kada kuri’a inda yake da masu kada kuri’a mutane miliyan 50.07.
Sai kuma yankin Kudu wanda yake da masu kada kuri’a mutane miliyan 43.23.