For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zaben 2023: Obasanjo Na Kokarin Zuga ‘Yan Kudu Don Kar Su Zabi Atiku, Yana Son Mulki Ya Koma Yankinsu

Ana tunkarar zaben shekarar 2023, tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya fara kiran manyan masu ruwa da tsaki a yankin Kudancin Najeriya da kar su goyawa dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Atiku Abubakar baya.

Majiyoyi na siyasa da suka tabbatar da yunkurin na Obasanjo sun ce, tsohon Shugaban Kasar wanda ya nuna rashin jin dadinsa da fitowar Atiku Abubakar takara a mai tsayawa PDP takarar Shugaban Kasa bayan ga ‘yan takara daga yankin Kudu sun fito takarar, inda ya ce shugabancin Najeriya ya kamata ya koma yankin Kudu bayan karewar wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari na shekaru takwas.

Atiku dai ya zama dan takarar jam’iyyar PDP ne a karo na biyu a zaben fidda gwanin da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, inda ya samu kuri’u 371 abin da ya ba shi damar doke abokin takararsa Nyesom Wike, wanda ya samu kuri’u 237.

Majiyoyin sun ce, rashin fahimtar da ke tsakanin Obasanjo da Atiku dai, ba ta rasa nasaba da dadaddiyar rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu tun lokacin da suna Shugaban Kasa da Mataimaki.

Sai dai kuma, Obasanjo ya ce ya yafewa Atiku inda kuma ya goyi bayansa a babban zaben da ya gabata na shekarar 2019 wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya kayar da Atikun.

Sai dai a wannan karon, Obasanjo na jin cewa gwara wani ya samu tikitin takarar a jamíyyar PDP maimakon tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar, kuma wannan shine dalilin da yasa yake neman jagororin Kudancin Najeriya da su juyawa Atiku baya a babban zaben shekarar 2023.

Wata majiya mai karfi da tai magana da LEADERSHIP kan abun da yake gudana a halin yanzu ta ce, tsohon Shugaban Kasar ya riga ya yiwa tsohon Gwamnan Jihar Cross River, Donald Duke da ya fara bin hanyar janyo hankalin manyan Kudu domin su kalubalanci Atiku.

Majiyar ta ce, cikin aikin da Donald Duke zai akwai neman goyon bayan mutanen Kudu ga takarar tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi wanda ya fito neman Shugaban Kasa a jam’iyyar Labour Party.

Haka kuma, Obasanjo ya gana da Peter Obi da kuma Donald Duke inda ya bukace su da su janyo hankalin Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, wanda ya nuna fushinsa bisa kayen da ya sha a hannun Atiku a zaben fidda gwanin da ya gabata.

Majiyar ta kuma baiyana cewa, Obasanjo ya gama shirye-shirye domin shi da kansa ya gana da Wike da kuma sauran manyan yankin Kudancin Najeriya domin tabbatar da cewa mulkin Najeriya ya dawo yankin a shekarar 2023.

Comments
Loading...