Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya ce ba za ta yiwu, a mika wa yankin kudancin kasar takarar shugaban kasa a jam’iyyar ba a zaben shekarar 2023 kawai saboda son kai ba.
Tsohon Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da BBC Hausa, inda ya ce ba laifi bane idan an yi hakan saboda tunanin zaman lafiya da kuma son farfado da tasirin jam’iyyar a yankin Arewa, wadda ake sa ran za ta karbi mukamin shugabancin jam’iyyar.
”Idan ma haka ta tabbata, sai dai a yi saboda zaman lafiya, misali akwai wadanda ke cewa yanzu PDP ba ta da karsashi a yankin Arewa, don haka akwai bukatar a samu wani daga yankin da aka tabbatar da sahihancinsa a bashi shugabancin don farfado da tasirinta, to idan an yi haka ba lafi bane, amma idan aka ce dole sai dai a kai Kudu, to wannan ba za ta yiwu ba” inji shi.
Ya kara da cewa ”ai an taba yin haka a PDP, aka dauko Obasanjo aka ce shi kadai zai yi takara, amma ka ga ai ba dole aka yi wa mutane ba, an yi ne domin ci gaban kasa da kuma son tabbatar da zaman lafiya da karuwar arziki”
BBC Hausa ta ce, da alama tsugune bata kare ba kan matsayar da kwamtin gwamnan Enugu ifeanyi Ugwuanyi ya gabatar ga jam’iyyar PDP na mika shugabancin jam’iyyar zuwa Arewacin kasar.
Ta rawaito cewa, wasu daga cikin kusoshin jam’iyyar na kalubalantar matakin inda suke ganin an shirya wa yankin makarkashiya ne don mayar da takarar shugabancin kasar ga yankin Kudu a shekarar 2023.
A wani martani da ya mayar kan ikirarin gwamnonin Kudu na dole mulki yam koma yankinsu, Kakakin Kungiyar Dattawan Arewa Dr Hakeem Baba Ahmed ya shaida wa BBC cewa Arewa tana da yawan masu zabe, don haka “yankin ba ya shakkar ko wace irin barazana.”
Su kuma gwamnonin Arewa sun mayar da martani ga takwarorin nasu ta hanyar cewa abin da gwamnonin Kudun suke fada ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.