Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da Cibiyar Gudanar da Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a ta Ngozi Okonjo Iweala ta gudanar, kuma Gidauniyar Atedo N. A. Peterside ta gabatar, ta nuna cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ne zai lashe zaben shugaban kasa a Najeriya in da za a gudanar da shi a yau.
Kuri’ar da aka gudanar a wannan watan ta nuna cewa, za a fafata takarar shugaban kasa ne a zabe mai zuwa tsakanin Peter Obi, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Bola Tinubu na jam’iyyar APC.
Kuri’ar ta kuma nuna cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya zo na hudu a kuri’ar a matsayin kurar baya.
Sakamakon ya nuna gagarumin rinjaye ga Peter Obi, inda ya samu kaso 21% na masu zabe idan har za a gudanar da zabe a yau; sai kuma kaso 13% wanda Atiku Abubakar da Bola Tinubu suka yi kunnen doki a kai a matsayin wadanda suka zo na biyu a kuri’ar.
Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya zo can baya a matsayin na hudu, masu kada kuri’ar kaso 3% ne suka nuna zasu zabe shi idan har za a gudanar da zaben shugaban kasar a yau.