For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

ZABEN 2023: Shekarau Ya Goyi Bayan Shugaban Kasa Ya Fito Daga Kudu

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, a ranar Litinin din nan ya ce, babu wani laifi idan dan Najeriya daga yankin Kudu ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Tshohon gwamnan ya goyi bayan hakan ne a yayin gabatar da shirin gidan talabijin na Channels mai suna Sunrise Daily.

Ya ce, yana son jam’iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) ta mika kujerar shugaban kasa zuwa Kudu.

Tsohon gwamnan ya yi amannar cewa juya ofishin shugaban kasa tsakanin Arewa da Kudu zai sa ‘yan kasar su ji cewa ana damawa da su kuma su bayar da gudunmawa wajen ci gaban kasa.

“Na taba fada a baya cewa, dangane da jam’iyyar da nake ciki ta APC, shawarata ita ce yanzu da Shugaba Buhari ya fito daga yankin Arewacin kasar, ya yi shekaru takwas, to a yanzu mu mayar da tunaninmu wajen zabowa wani daga Kudancin Najeriya,” in ji shi.

“Ba wai saboda ba mu da isassun mutane da suka cancanta a Arewa ba. Idan ka ce ‘bari bangare daya na Nijeriya ya samar da jagora,’ wannan ba yana nufin kowanne kare ma ya nema ba, a a akwai batun kwarewa, batun amana, da sauransu.

“Duk da cewa na yarda yakamata mu samar da mafi inganci, saboda haka, a bude damar ba tare da la’akari da ko wane bangare na kasar ba mutum ya fito ba, ya kamata mu ma mu kula da sanyawa ‘yan kasa cewa su ma a na yi da su. Kun ga, dole ne mu tuna da irin wannan tsinkaye don ba da damar ga kowane yanki na Najeriya.”

An jima ana tafka muhawara kan karba-karbar kujerar shugaban kasa tsakanin Kudu da Arewa, kuma su ma gwamnonin jihohi ba a bar su a baya ba wajen nuna inda suke so abin ya karkata.

A lokacin da Shugaba Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu, Kungiyar Gwamnonin Kudu na son wanda zai gaje shi ya fito daga yankin Kudu.

Kungiyar gwamnonin Arewa, a martanin ta, ta ce kundin tsarin mulki bai wani tanadi game jujjuya ofishin Shugaban kasa tsakanin yankuna biyu ba.

Duk da cewa gwamnonin Arewa ba sa adawa da kiran da ake yi na shugabanci na shiyya, amma sun yi tir da matakin da abokan aikinsu na Kudu suka dauka.

“Na yarda da ra’ayin cewa ya kamata mu yi maganar Arewa da Kudu, amma inda na saba da gwamnonin kudu sun hadu sun ce‘ dole ne ’; Ina ganin wannan magana ce kawai ta jam’iyya,” in ji Shekarau.

Comments
Loading...