Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya yi zargin cewa, wasu daga cikin masu adawa da shi na son Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kalubalance shi a lokacin zaben fitar da gwani.
Tinubu ya fadi hakan ne lokacin da yake mayar da martani kan abin da ya biyo bayan jawabin da ya yi wa delegets a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun a ranar Alhamis da ta gabata.
A lokacin, Tinubu, ya kalli Gwamnan Jihar Ogun, inda ya baiyana karara ta hanyar kiransa da sunansa, ya ce shi ya temake shi ya zama gwamna.
Ya fadi hakan ne bayan ya baiyana karara cewar, gwamnan ya ki ya goyi bayan Tinubun kan kudirinsa na zama Shugaban Kasa a shekarar 2023.
Sai dai kuma a jawabin da ya saki a jiya Juma’a, Tinubu ya ce, masu adawa da shi sun juya maganganunsa na Abeokuta ne domin su nuna cewar ya yi wa Buhari gori, da fatan hakan ya sa Shugaban Kasa ya kalubalanci takararsa a zaben fitar da gwani.
Ya kuma tabbatar da cewa, zai amince da sakamakon zaben fitar da gwanin da APC zata gudanar a tsakanin ranakun 6 zuwa 8 ga watan Yuni a Abuja.
Tinubu ya ce, ya yi maganganun da yai ne a Abeokuta bayan farmakin da ake yi wa mutuntakarsa a matsayin yakin neman zaben sauran ‘yan takarar Shugaban Kasa, inda ya ce ya yi hakan ne domin ya tunawa wadanda ba su san tarihin jam’iyyar APC su sani.
“Bari in cire muku shakku. Girmamawata da mutuntawa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayinsa Shugaban wannan kasa da kuma a matsayinsa na shi kan sa suna da girma kuma ba zan daina ba. Ba zan taba ci masa mutunci ba. Ban yi haka ba a Abeokuta. Mun kasance abokan siyasa na tsawon lokaci kuma ina fatan wannan abokantaka ta ci gaba yanda ya kamata a nan gaba. Ba zan taba yin abin da zai lalata ta ba,” in ji Tinubu.